Kamfanin Dillancin Labarain ƙasa da ƙasa Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: An fitar bidiyon farko na mutuwar 'yan ta'addar Iranshahr kamar yadda Hedikwatar Rundunar Quds ta IRGC ta sanar da kashe wasu daga cikin 'yan kungiyar ta'addanci a Sistan da Baluchestan.
A hare-haren hadin gwiwa guda 3 tare da hadin gwiwar Farajah da Sojojin Imam Zaman (a.s.) a Iranshahr, Khash da Saravan, an kashe 'yan ta'adda 13 tare da kama wasu da dama.
Kakakin Farajah: 8 daga cikin 'yan ta'addan da aka kashe sun su suka aiwatar da shahadantar da jami'an tsaro 5 a yankin "Daman" na IranShahr a makon jiya.
Sardar Montazer al-Mahdi: A wannan farmakin an gano makamai da alburusai tare da kwace su.
Your Comment